Gwamnatin jihar Kano ta ware naira miliyan 80 domin gyara magudanan ruwa don kare ambaliya

A wani yunkurin da gwamnatin jihar Kano takeyi domin magance ambaliyar ruwa a fadin jihar, yanzu haka sun ware kimanin naira miliyan 80 domin gyara magudanan ruwa dake lungu da sakon kano.

Kwamishinan muhalli na jihar Dr. Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kaddamar wani tsarin da aka yi masa LAKABI da KANO TSAF TSAF na 2021, domin tabbatar da tsaftar jihar.

Getso kazalika ya bukaci al’umma da su daina zubar da shara a magudanan ruwa, domin ruwa yake samun damar ficewa batare da tangarda ba.

Ya karar da cewa dole sai gwamanatin da al’umma sunzama tsintsiya madaurin ki kafin a samo bakin zaren matsalar ambaliyya

Awani labarin kuma gwamnatin jihar kanon ta samar da kayan ayyukan gyaran muhalli ga wurare 100 a fadin jihar kanon.

Kayan gyaran muhallin sunhada da shebir, manjagara, diga, Baro dadai sauransu.

Comments (0)
Add Comment