Gwamnatin kasar Algeria za ta fara biyan tallafin rashin aikin yi sama da 41,000 ga matasa masu tasowa

Gwamnatin kasar Algeria za ta fara gabatar da tallafin rashin aikin yi ga matasa masu tasowa a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar rashin ayyukan yi.

Shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune ya shaida wa manema labarai cewa za a fara biyan matasa marasa aikinyi daga shekaru 19 zuwa 40 tindaga watan Maris din wannan shekarar

Wadanda suka cancanta za su na samun Dalar amurka $ 100 kimanin naira dubu 41,700 a kowanne  wata, da kuma wasu fa’idodin kiwon lafiya, har sai sun sami aiki.

Da yake bayyana hakan, Mista Tebboune ya ce Algeria ce kasa ta farko a wajen Turai da ta bullo da irin wannan kudirin mai mahimmancin gaske.

Ya kara da cewa yanzu haka akwai marasa aikin yi sama da 600,000 a Aljeriya.

Comments (0)
Add Comment