

Gwamnatin kasar Algeria za ta fara gabatar da tallafin rashin aikin yi ga matasa masu tasowa a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar rashin ayyukan yi.
Shugaban kasar Abdelmadjid Tebboune ya shaida wa manema labarai cewa za a fara biyan matasa marasa aikinyi daga shekaru 19 zuwa 40 tindaga watan Maris din wannan shekarar
Wadanda suka cancanta za su na samun Dalar amurka $ 100 kimanin naira dubu 41,700 a kowanne wata, da kuma wasu fa’idodin kiwon lafiya, har sai sun sami aiki.
Da yake bayyana hakan, Mista Tebboune ya ce Algeria ce kasa ta farko a wajen Turai da ta bullo da irin wannan kudirin mai mahimmancin gaske.
Ya kara da cewa yanzu haka akwai marasa aikin yi sama da 600,000 a Aljeriya.