Gwamnatin Jigawa ta jadadda kudirinta na daukar kwararan matakai na rage talauci a jihar

0 150

Dangane da haka ne gwamnati ta samar da isassun kudade ta hannun hukumar kula da masu bukata ta musamman domin kula da masu rangwaman gata da kuma kara yawan masu bukata ta musamman da kuma alawus alawus da suke samu a kowane wata.

Kwamishiniyar alamurran mata da jin dadin jama-a ta jiha , Hajia Hadiza AbdulWahab ta sanar da hakan a lokacin da suka kai ziyarar ban girma ga masu martaba sarakunan Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje da kuma na Gumel, Alhaji Ahmed Muhammad Sani.

A fadar maimartaba sarkin Gumel, Hajia Hadiza Abdulwahab ta ce suna ziyartar sarakunan ne domin sanar dasu manufofin gwamnati na kididdigar marayu da masu karamin karfi da tsofaffi da kungiyoyin taimakawa marayu da masu bukata ta musamman.

Tace gwamnati tana da niyyar kara adadin masu bukata ta musamman da suke amfana da alawus na wata-wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: