Hukumomi na aiki da jami’an tsaro wajen kamo duka ragowar fursunoni 109 da suka tsere daga gidan gyaran hali

0 91

Hukumomi a Najeriya sun ce suna aiki tare da jami’an tsaro wajen kamo duka ragowar fursunoni 109 da suka tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja.

Ministan cikin gida, Dakta Olubunmi Tuni-Ojo ne ya bayar da tabbacin lokacin da ya kai ziyara gidan yarin domin duba irin ɓarnar da ruwan sama ya yi wa ginin abin da ya bai wa fursunoni 119 dama ta tserewa ranar Laraba da daddare.

Bayan tserewar fursunonin ne kuma aka yi nasarar kamo 10 a cikinsu.

Tunji Ojo, bisa rakiyar shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali a Najeriya, Halliru Nababa, ya ce gwamnati za ta sauyawa gidan yarin mazauni saboda yadda yanzu ya kasance cikin al’umma.

A cewar hukumomin gidan yarin, wurin na tsakiyar gidajen jama’a kuma an gina shi tun 1914. Ministan ya amince cewa ginin daɗaɗɗe ne.

Minisitan ya ce kafin faruwar lamarin, gidan yarin na ɗaukan fursunoni 499, adadin daya zarce yawan mutum 250 da aka tsara ya ɗauka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: