Za’a gudanar da cikakken bincike don tabbatar da ingancin duka jiragen sama da ke zirga-zirga a Najeriya

0 193

Gwamnatin Najeriya ta ce hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama a Nijeriya za ta gudanar da cikakken bincike don tabbatar da ingancin duka jiragen sama da ke zirga-zirga cikin ƙasar.

Ministan sufuri Festus Keyamo ne ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis.

Ya ce baya ga dakatar da kamfanin Dana da kuma binciken da ake yi wa kamfanin, za a gudanar da bincike a kan duka kamfanonin jiragen sama a ƙasar domin tabbatar da bai wa fasinjoji kariya.

A ranar Laraba ne, Keyamo ya ba da umarnin dakatar da kamfanin na Dana inda ya ce abubuwan da suka faru da jirgin a baya-bayan nan sun saka damuwa a zukatan jama’a.

An dakatar da kamfanin Dana kwana ɗaya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga kan titinsa a filin jirgin saman Legas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: