Cibiyar ICAN ta karrama Gwamna Mallam Umar Namadi na Jihar Jigawa da lambar yabo

0 225

Cibiyar Kula da Akantoci ta kasa (ICAN) ta ba Gwamna Mallam Umar Namadi na Jihar Jigawa lambar yabo bisa la’akari da jajircewarsa na inganta gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari.

A wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Kwamared Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, ya ce an ba gwamna Namadi lambar yabon ne a lokacin bikin cin abinci da kyaututtuka na 2024 da aka gudanar a yammacin ranar Asabar a Legas.

A lokacin da yake mika lambar yabo ga gwamnan shugaban kungiyar ICAN, Dokta Innocent Okwuosa ya ce kungiyar a matsayinsa na kwararru ne kawai ta karrama mutanen da suka nuna himma wajen inganta gaskiya, rikon amana, aiki tukuru da kuma shugabanci na gari.

A nasa jawabin jim kadan bayan karbar lambar yabon, Namadi ya mika godiyarsa ga hukumar gudanarwa ta ICAN.

Leave a Reply

%d bloggers like this: