Gwamna jihar kano Abba Kabir Yusuf ya musanta korar duk wasu masu aikin tsaftace titi da masu shara kamar yadda ake ta yadawa a sassa daban-daban na jihar.
Gwamnan na kano ya musanta hakan ne a jiya Lahadin yayin wata ganawa da ya yi da wakilan masu sharar a gidan gwamnati.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen ganin an samar da tsaftataccen muhalli da lafiya domin jin dadin mazauna jihar.
Abba Kabir ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden alawus-alawus na wadanda da suka gada daga gwamnatin da ta gabata.
Da yake yaba musu kan hakuri da jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka, ya bukace su da su ci gaba da mayarwa da gwamnati alheri ta hanyar rikon amana da aiki tukuru.