Gwamnatin jihar Katsina ta ce ta dauki karin ma’aikata kusan 304 a hukumar kula da ababen hawa ta jihar, KASROTA.
Darakta Janar na hukumar, Manjo Garba Yahaya-Rimi mai ritaya ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasa a Katsina.
Yahaya-Rimi ya bayyana cewa daukar ma’aikatan an yi shi ne domin a karfafa kwazon ma’aikatan hukumar domin samun kyakkyawan aiki wajen rage cin hanci da rashawa da masu amfani da tituna ke yi a jihar.
Mista Yahaya-Rimi ya ce a yanzu haka ma’aikatan su na nan a fadin kananan hukumomi 13 daga cikin 34 na jihar.
Ya tunatar da masu amfani da hanyar cewa hukumar KASROTA ba a kafa ta ne a matsayin hanyar samun kudaden shiga ba, an kafa ne don tabbatar da tsaron rayukan jama’a.