Ministan ilimi na Kasa Malam Adamu Adamu, ya ce matakin yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) na wata daya abin mamaki ne.

Ya ce ba laifin gwamnatin tarayya ba ne idan har ba a cimma matsaya ba bayan tattaunawa da dama tsakanin bangarorin biyu.

Ministan ya yi wannan magana ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Adamu ya ce ASUU ta yanke shawarar shiga yajin aikin ne ba zato ba tsammani a dai dai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa.

A cewarsa, wani kwamiti yana dubawa. Idan ya kammala, gwamnati a shirye take ta sanar ta amince, inda ya kara da cewa kwatsam ya ji sun tafi yajin aiki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: