Gwamnonin jahohin arewacin Najeriya sun bayyana damuwa bisa cigaba da karuwar matsalolin sace-sacen jama a, da rashin shigar yara makaranta rashin tsaro da sauran matsalolin da suke da nasaba da shiyyar.
Yayin taron da suka gudanar jiya talata 30 ga watan Aprilu a garin Kaduna, gwamnonin sun ce hakika wadannan jerin matsaloli sune suke dakile cigaban shiyyar, kuma wajibi ne a shawo kansu.
Wannan taro dai shine karo na biyu da gwamnonin suka gudanar cikin shekara guda.
Da yake jawabi, shugaban kungiyar gwamnonin na arewa kuma gwamnan jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce, muddin dai ana bukatar shiyyar arewa ta fita daga cikin wadancan matsaloli sai dole an kyautata sha`anin tattalin arziki da bullo da matakan gina al`umma.
Ya ce yanzu arewacin Najeriya shi yafi kowanne bangare a duniya yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, inda ya ce hakan kalubale ne babba da ke gaban gwamnonin shiyyar wajen ganin an yiwa tufkar hanci cikin gaggawa