Yan daba sun kashe matafiya hudu a mahadar Bida Bidi da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato

0 101

Yan daba sun kashe matafiya hudu a Mahadar Bida Bidi da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

An kai wa matafiyan da suka taso daga Jihar Kano za su ce Jihar Nasarawa harin ne da misalin karfe 12 na daren Laraba, aka jikkata da dama daga cikinsu.

’Yan daba sun tare matafiyan ne a kan titin Zariya Road, inda suka sassari wasu da adduna, suka kashe wasu, suk akona motar da matafiyan, sannan suka fasa gilasan wasu motoci.

An garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin Bingham da ke garin Jos, inda suke samun kulawa.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Filato, ASP Uba Gabriel, ya tabbatar da rasuwar mutum biyu a sakamakon harin, yana mai cewa Kwamihinan ’yan sandan kihar ya ziyarci wurin da abin ya faru domin tabbatar da bin doka da oda.

An kai wa matafiyan harin ne awanni kadan bayan an kai wa masu hakar ma’adinai hari aka kashe biyu daga cikinsu a wani wurin hakar ma’adinai da ke yakin Yelwan Zagam a ranar Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: