

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya bukaci masu shirya fina finan Hausa da su kiyaye da kaidoji da dokoki da aladu da kuma addinin mutanen jihar jigawa
Ya yi wannan kiran ne a lokacin da mai shirya wasan hausa na Kwana Casa’in a tashar talabijin ta Arewa 24 ya ziyarci ofishinsa
Mallam Umar Namadi yace gwamnatin jiha a shirye take wajen tallafawa duk wata kungiya da take da Muradin dabbaka aladu da Muradin alummar jihar nan
Ya kuma yi gargadin cewar gwamnati ba zata laminci duk wani abu da ka iya zubar da kima da kuma mutuncin jihar da alummar jihar nan baki daya
Tun farko a jawabinsa babban jamiin shirya wasan Hausa na Kwana Casa’in, Mr Evans Ejiogu yace sun ziyarci ofishin mataimakin gwamna ne domin godewa gwamnati bisa hadin kai da goyan bayan da take basu wajen shirya Shirin Kwana Casa’in a jihar jigawa
Inda ya bada tabbacin cigaba da kiyayewa da dokoki da kuma kaidojin da aka shimfida musu