Gwamnatin tarayya ta buƙaci ma’aikatan ta masu matakin albashi na 12 da su koma bakin aiki

Gwamnatin tarayya ta bukaci Ma’aikatan ta masu matakin Albashi na 12 su koma bakin aiki daga ranar 1 ga watan Disamba.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin tarayya Dr Folasade Yemi-Esan, ita ce ta bayyana hakan, inda ta ce hakan ya biyo bayan umarnin Kwamatin yaki da cutar Corona na Shugaban Kasa.

A wani mataki na rage yaduwar cutar Corona, Gwamnatin tarayya a ranar 4 ga watan Maris ta umarci Ma’aikata masu matakin Albashi na 12 zuwa kasa su fara aiki daga gida.

Bayan Kimanin watanni 8 kenan, gwamnatin tarayya ta umarci Ma’aikata su gabatar da shaidar anyi musu rigakafin cutar Corona cikin a wanni 72 masu zuwa.

Dr Folasade Yemi-Esan, ta bayyana cewa kowanne ma’aikaci ya tabbatar da cewa an mssu rigakafin cutar, kamar yadda Kwamatin Shugaban Kasa kan yaki da cutar Corona ya bukata.

Comments (0)
Add Comment