Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da cire harajin Naira 10 ga kowace lita a kan duk wani abin sha da baya dauke da sinadarin barasa

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da cire harajin Naira 10 ga kowace lita a kan duk wani abin sha da baya dauke da sinadarin barasa, da kuma masu zaki.

Wannan din dai a matsayin wani nau’in haraji da aka sanya akan izinin samarwa, da izini da siyar da kaya.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 ga jama’a jiya Laraba a Abuja.

A cewarta, sabuwar manufar da aka bullo da ita tana cikin dokar kudi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a ranar 31 ga watan Disamba, 2021 ta bara.

Har ila yau, ministar ta ce gwamnati ta bullo da wata doka da ta bukaci kamfanonin kasashen waje da ke kasuwanci a kasar nan su karba tare da mika haraji ga Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya.

A cewarta, sabuwar manufar tana kuma kunshe ne a sashe na 30 na dokar kudi da ta yi wa tanadin sashe na 10, 31 da 14 na harajin ga kamfanonin yanar gizo da ba na kasar nan ba.

Comments (0)
Add Comment