Ministan ayyuka, Babatunde Fashola, ya sanar da haka lokacin da yake gabatar da tsare-tsaren shirin ga hadakar kwamitocin ayyuka na majalisun kasa.
Ministan yace masu zuba jari zasu gudanar da aiki da kula da manyan titunan.
- Gwamnatin Sokoto Ta Bai Wa Sojojin Najeriya Gudummuwar Motocin Sulke 62
- Guguwar Iska Ta Kashe Mutane Uku, Ta Lalata Gidaje Da Ababen More Rayuwa A Yobe
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Takwas, Sun Kwato Makamai A Katsina
- Gwamnan Zamfara: Na Ƙi Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 300, Na Ce Su Kashe ‘Yan Uwana
- EFCC Ta Gurfanar da Bello Bodejo Kan Zargin Badaƙalar Kuɗi
- Ma’aikatan Abuja Ba Sa Sona — Wike
Fashola yace Zangon farko na aiki zai lakume kudi naira biliyan 163 da miliyan 320, akan kimanin naira biliyan 16 domin kowane titi guda daga cikin goman.
Titunan sune na Benin zuwa Asaba, Abuja zuwa Lokoja, da Kaduna
zuwa Kano, da Onitsa zuwa Owerri zuwa Aba, da Shagamu zuwa Benin, da Abuja zuwa
Keffi zuwa Akwanga, da Kano zuwa Maiduguri, da Lokoja zuwa Benin, da Enugu zuwa
Fatakwal da kuma Ilorin zuwa Jebba.