Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Shirin Mika ikon kula da Manyan Titunan Kasarnan Ga Masu Zuba Jari

0 72

Ministan ayyuka, Babatunde Fashola, ya sanar da haka lokacin da yake gabatar da tsare-tsaren shirin ga hadakar kwamitocin ayyuka na majalisun kasa.

Ministan yace masu zuba jari zasu gudanar da aiki da kula da manyan titunan.

Fashola yace Zangon farko na aiki zai lakume kudi naira biliyan 163 da miliyan 320, akan kimanin naira biliyan 16 domin kowane titi guda daga cikin goman.

Titunan sune na Benin zuwa Asaba, Abuja zuwa Lokoja, da Kaduna zuwa Kano, da Onitsa zuwa Owerri zuwa Aba, da Shagamu zuwa Benin, da Abuja zuwa Keffi zuwa Akwanga, da Kano zuwa Maiduguri, da Lokoja zuwa Benin, da Enugu zuwa Fatakwal da kuma Ilorin zuwa Jebba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: