

Kwamishinan kare mahalli na jiha Alhaji Ibrahim Baba Chai-Chai ya sanar da hakan a lokacin da yake bayani kan bikin ranar mahalli da yaki da kwararowar hamada ta bana.
Yace za a raba dashen itatuwan ne ga al’umma kyauta domin dasawa a masallatai da gonaki da asibitoci da makarantu da kuma sauran wuraren taruwar jama’a.
- Tarihin Gamuwa 10 Tsakanin Kano Pillars VS Eyimba Da Kuma Wasan Yau
- Abubuwa 5 da suka zama wajibi lokacin sanyi
- An ƙaddamar da kudin kariya ga ƴan jarida da masu fafutukar ƴancin amfani da yanar gizo
- Yadda ake duba suna don zama ma’aikacin damara na 2020 a Nijeria
- Me Ƙungiyar Izala ta ce kan matsalolin tsaro a Najeriya?
Baba Chai-Chai yayi kira ga jama’a da su marawa kudirin gwamnatin jihar baya na yaki da kwararowar hamada da zaizayar kasa.
A nasa bangaren, daraktan dazuka na ma’aikatar, Alhaji Haladu Bulama, yayi kira ga masu sarautun gargajiya da kungiyoyin sa kai da su hada kai da ma’aikatar wajen tabbatar da aiwatar da shirin kamar yadda ya kamata.