Karar Kwana: Tsawa Ta Kashe Jami’an Kiyaye Haddura A Nijeria

0 70

Tsawa a jiya Laraba ta kashe jami’ai 3 na hukumar kiyaye hadura ta kasa, dake aiki da reshen hukumar na jihar Ogun.

Ance tsawa ta fada kan jami’an a ofishinsu dake tsohon toll gate a Ilese, yankin karamar hukumar Ijebu ta Arewa da Gabas, dake jihar.

An gano cewa lamarin ya auku da misalin karfe 10 na safe lokacin da jami’an hukumar ke shirin atisayen safiya.

Jami’ar ilimintar da jama’a ta hukumar kiyaye hadura, reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Okpe, sai dai, tace har yanzu ba a san musabbabin mutuwar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: