Gwamnatin Tarayya ta samu nasarar dakile tafiya yajin aiki sama da sau dubu 4

Gwamnatin Tarayya tace ta samu nasarar dakile tafiya yajin aiki sama da sau dubu 4 daga kungiyoyin ma’aikata a fadin kasarnan ta hanyar tattaunawar sulhu cikin shekaru 7 da suka gabata.

Ministan kwadago da aikin yi, Dr Chris Ngige, shine ya sanar da haka a wajen taron manema labarai na ministoci da ake yi sau biu kowane sati wanda tawagar sadarwar shugaban kasa ta shirya jiya a Abuja.

A cewarsa, tattaunawar sulhu ita ce hanya mafi kyau wajen sassanta rikicin kwadago.

Chris Ngige ya kara da cewa ma’aikatar na da teburan sassan rikicin kwadago da bayar da daukin gaggawa a dukkanin jihohin kasarnan wadanda suka taimaka wajen magance rikice-rikicen ma’aikata.

A cewar ministan, tuni aka fara tsare-tsaren karin albashi ga ma’aikata musamman wadanda ke karbar alawus-alawus na musamman, inda ya kara da cewa hukumomi na jiran amincewar shugaban kasa ne kadai domin fara aiwatarwa. Ministan ya kara sanar da cewa Najeriya ta kammala shirye-shiryen hada kai da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya domin hana ‘yan kasarnan tafiya neman aiki kasashen waje ba bisa ka’ida ba.

Comments (0)
Add Comment