Gwamnatin tarayya tace an bullo da shirin inganta rayuwar alumma ne da nufin rage kaso 70 na talauci da yan Najeriya ke ciki

Gwamnatin tarayya tace an bullo da shirin inganta rayuwar alumma ne a 2016, da nufin rage kaso 70 na talauci da yan Nigeria ke ciki.

Ministar jinkai da kula da jindadin jama-a ta kasa Hajia Sadiya Umar Farouk, ta bayyana hakan a wajen bikin kaddamar da shirin bunkasa kananan sanaoi na gwamnatin tarayya a jihar Jigawa.

Ministar wadda ta samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar, Dr Nasiru Sani Gwarzo tace an yiwa mutane dubu 48,000 rijistar shiga shirin a jihar nan daga 2017 zuwa yanzu.

Inda kowannensu ya samu rancen naira dubu hamsin marar kudin ruwa daga gwamnatin tarayya domin fara sana-a.

An raba shirin kaso uku da suka hadar da na Trader money da Market money da kuma farmers money.

A sakon daya aike dashi wajen bikin, gwamna Muhammad Badaru Abubakar ta hannun shugaban ma’aikata, Alhaji Hussain Ali Kila ya yabawa gwamnatin tarayya bisa tallafawa jihar Jigawa a tsare tsarenta na yaki da fatara da talauci.

Comments (0)
Add Comment