‘Har yanzu ina kan matsayata da a dena kwatanta ayyukana da na sauran gwamnoni’ -Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni su daina.

Ya yi rokon ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gasau ya fitar jiya Litinin.

Gwamnan ya yabawa mutanen da ke tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da bambanci.

Amma yana matukar godiya bisa dukkan goyon baya da tallata ayyukansa da mutane sukeyi a kwanakin nan.

Ya kuma ce yana samun sakonni, inda ake kwatanta ayyukan da da yakeyi yi a Borno da cewa sun zarta na wasu jihohi.

Ya kara da cewa Gaskiya bayajin dadi a duk lokacin da aka kwatanta shi da wani gwamna ta hanyar muzanta shi, musamman idan wadanda suke yin hakan suna cikin masu amfani da shafukan sada zumunta.

Comments (0)
Add Comment