Hukumar Asusun Adashen Gata na ma’aikatan jihar Jigawa ta raba Naira biliyan 4 ga ma’aikata 12,000 da 868 da suka yi riyata

Hukumar Asusun Adashen Gata na Ma’aikatan Jiha da n Kananan Hukumomi ta ce ta raba Naira Biliyan 4 ga Ma’aikata Dubu 12 da 868 da suka yi Riyata cikin shekara 6.

Sakataren Zartarwa na Hukumar Alhaji Kamilu Aliyu Babura, shine ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi karkashin Jagorancin Mista Ambali Akeem wanda suka kawo masa ziyara a Ofishin sa.

A cewarsa, kudaden sun kunshi biyan hakkokin Ma’aikatan da suka yi ritaya da wanda suka mutu da kuma kudaden Fansho na Alawus-Alawus daga shekarar 2015 zuwa 2022.

Kazalika, ya ce kudaden sun hada da Ma’aikatan Jiha da na Kananan Hukumomi da kuma na Sashen Ilimi na Karamar Hukuma.

Comments (0)
Add Comment