Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gargadi al’ummar Musulmi da su guji kin yin azumin watan Ramadan da gangan

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gargadi al’ummar Musulmi da su guji kin yin azumin watan Ramadan da gangan.

A wani sakon murya ta WhatsApp da ya aika wa kungiyoyin yada labarai a Kano, kwamandan hukumar Hisbah na jihar, Haroun Ibn-Sina, ya ce hukumar ba za ta kyale duk wanda aka samu yana cin abinci da rana ba tare da wani kwakwakwaran dalili ba.

A cewarsa, hukumar Hisbah ba za ta nade hannunta tana ganin yadda matasa musulmi ke keta hurumin addinin Musulunci a jihar ba, musamman a wannan wata mai alfarma, inda ake bukatar musulmi su gudanar da cikakkiyar ibada ga Allah.

Haruna Ibn-Sina ya kara da cewa, hukumar Hisbah ba za tayi kasa a gwiwa ba, wajen gudanar da aikinta na tabbatar da cikakken bin tsarin shari’ar Musulunci a cikin watan Ramadan da ma bayansa, inda ya ce duk wanda aka samu yana saba wa Shari’a, za a hukunta shi.

Haruna Ibn-Sina ya jaddada cewa Hisbah ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na yaki da badala a Kano.

Comments (0)
Add Comment