Hukumar INEC ta gano sama da mutane milyan daya da sukayi rijistar katin zabe ba bisa cancanta ba

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gano wasu mutane da suka yi rijista sau biyu zuwa sama da wadanda rijistarsu ba ta cancanta ba, a cikin kundin rajistar masu kada kuri’a da aka ci gaba da yi tsakanin ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Yuli.

Kwamishinan hukumar INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Ya bayyana cewa an gano kura-kuran a lokacin tsaftace rajistar masu kada kuri’a ta hanyar amfani da na’urar tantancewa ta ABIS.

A baya dai hukumar ta bayyana cewa daga cikin rajistar mutane miliyan 2 da dubu 523 da 458 da aka yi tsakanin ranar 28 ga watan Yunin 2021 zuwa ranar 14 ga watan Junairun 2022, an gano sunayen masu rajista miliyan 1 da dubu 126 da 359 ba su da inganci kuma aka yi watsi da su.

Comments (0)
Add Comment