Hukumar jin dadin Alhazai zata gudanar da bita ga sabbin jamianta na kananan hukumomi

Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Jigawa zata gudanar da taron bitar sanin makamar aiki ga sabbin jamianta na kananan hukumomi wato center officers. 

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin hukumar Murtala Usman Madobi ya sanyawa hannu.

Yace za a gudanar da bitar ne a ranar Talata shida ga watan Fabrairu a dakin taro na kungiyar maaikatan lafiya ta jihar Jigawa dake Dutse. Sanarwar ta kara da cewar za a gudanar da taron bitar ne karkashin jagorancin Darakta Janar na Hukumar Alhaji Ahmad Umar Labbo.

Comments (0)
Add Comment