Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jiha (JISEPA) ta kaddamar da aiki tsaftar muhalli na kwanaki goma a kananan hukumomi hudu dake yankin masarautar Hadejia

Hukumar kula da tsaftar muhalli ta jiha (JISEPA) ta kaddamar da aiki tsaftar muhalli na kwanaki goma a kananan hukumomi hudu dake yankin masarautar Hadejia.

Manajan daraktan hukumar, Injiniya Lawal Ahmed Zauma, ya bayyana haka a yayin kaddamar da aikin a garin Guri.

Yace aikin ya ka su kashi biyu wanda ya hada da kwashe shara a unguwanni da kasuwanni da yin feshin maganin sauro a makarantun kwana da asibitoci da kuma sauran gine-ginen hukumomin gwamnati.

Lawal Ahmed Zauma, ya ce manufar aikin itace tsaftace garuruwa domin kare al’umma daga kamuwa daga cututtuka masu yaduwa a sanadiyyar rashin tsaftar muhalli.

Manajan daraktan ya bukaci al’umma, musamman shugabannin kananan hukumomin Guri da Malam-Madori da Auyo da Hadejia da kungiyoyin ‘yan kasuwa dana kyautatatuwar zaman jama’a da su mara baya ga ma’aikatan hukumar, domin cimma nasarar tsaftace yankunan kananan hukumomin su.

Comments (0)
Add Comment