Hukumar NDLEA ta kama ma’aikatan tsaro na bogi 2 dauke da tabar wiwi rol 25 da kuma kwalba dubu 1,598 na codeine

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta bayyana cewa Jami’an ta sun kama Ma’aikatan tsaro na Bogi 2 dauke da tabar wiwi Rol 25 da kuma Kwalba dubu 1,598 na Maganin Tari wato Codeine a Jihar Yobe.

Daraktan Hulda da Kafafen Yada Labarai na Hukumar Mista Femi Babafemi, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya.

Sanarwar ta ce Mutanen da aka kama sun hada da Akalonu Justin da kuma Azimbi Festus, kuma an kama sune a lokacin da suka fito daga Onitsha domin zuwa Maiduguri na Jihar Borno.

Hukumar ta ce ta yi nasarar gano wata tabar wiwi mai nauyin Kilogram 85 a wani wurin ajiya mallakin Dilan kwayoyi da ke Pawari a birnin Damaturu na Jihar Yobe.

Shugaban Hukumar na Kasa Birgediya Janar Muhammed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya yabawa Jami’an hukumar kan yadda suke gudanar da ayyukan su cikin kwarewa a kokarin da suke yi wajen ganin sun dakile safarar kwayoyi.

Comments (0)
Add Comment