Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi gargadin cewa babu wani mutum da zai yi zabe matukar ba’a tantance shi ba

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta yi gargadin cewa babu wani mutum da zai yi zabe matukar ba’a tantance shi.

Sabon Kwamishinan Hukumar a Jihar Jigawa Farfesa Muhammad Lawan Bashar, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse.

A cewarsa, hukumar zata fara Kafe Rijistar masu zabe daga ranar 12 zuwa 25 ga watan Nuwamba na wannan shekara.

Kwamishinan Hukumar ya ce za’a kafe Rijistar a dukkanin Mazabu da Kananan Hukumomin Jihar Jigawa.

Haka kuma ya ce kafe Rijistar zai bawa mutane damar gano sunayen da suka yi amfani da shi a lokacin Rijistar zaben.

Farfesa Lawan Bashar, ya shawarci mutane su ziyarci Mazabun su da Kananan Hukumomin su domin ganin hotunan su da kuma sunayen da zasu bayyana a jikin katunan zaben su.

Comments (0)
Add Comment