Yawan mutanen da annobar corona ta shafa a Najeriya ya kai dubu arba’in da tara da dari takwas da casa’in da biyar, bayan an sake gano mutane dari hudu da goma dauke da cutar a jiya.
Daga cikin adadin, sama da mutane dubu talatin da bakwai sun warke kuma an sallamesu a jihoshi talatin da shida na kasarnan, da babban birnin tarayya, Abuja.
- Ya Kamata A Kyautata Rayuwar Talaka Bayan Cire Tallafin Mai – Atiku
- An Kama Mai Safarar Bindigogi A Tashar Mota A Zariya
- Alƙawarin Atiku Na Dawo da Tallafin Mai Ya Jawo Muhawara A Jigawa
- Tun da Na Zama Gwamnan Kaduna Ban Karɓi Bashin Sisin Kobo Ba – Uba Sani
- ’Yan Bindiga Sun Kashe Malami, Sun Sace Mutum 10 A Sakkwato
Cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu cikin sa’o’i ashirin da hudu, kuma yawan wadanda annobar ta kashe kawo yanzu ya kai dari tara da tamanin da daya.
Hakan ya fito ne daga hukumar dakile yaduwar cututttuka ta kasa NCDC, wacce ke jagorantar kula da barkewar cutar corona, cuta mai kama da mura, wacce ta yadu zuwa kasashe sama da dari biyu kuma ta harbi sama da mutane miliyan biyu.