Jadawalin Gasar Kofin Duniya Ta 2026

An fitar da jadawalin wasannin Gasar Kofin Duniya ta 2026 da za a gudanar a ƙasashen Amurka da Mexico da Canada, wadda za ta fara a ranar 11 ga watan Yuni, 2026.

Za a fara gasar ne da wasan rukuni na A tsakanin Mexico da Afirka ta Kudu a birnin Mexico City ranar Alhamis, 11 ga watan Yuni da ƙarfe 7:00 na yamma agogon GMT.

A rana guda kuma, Koriya ta Kudu za ta kara da Jamhuriyyar Czech a birnin Guadalajara.

A ranar Asabar 13 ga watan Yuni, za a fafata tsakanin Brazil da Morocco a birnin East Rutherford.

Ita kuwa Jamus za ta kara da Curacao, yayin da Netherlands za ta fafata da Japan a ranar Lahadi 14 ga watan Yuni.

Sai kuma Spain da za ta kara da Cape Verde, yayin da Belgium za ta kara da Masar a ranar Litinin 15 ga watan Yuni.

Ƙasashen Afirka da za su haska a gasar
Daga cikin ƙasashen Afirka da za su fafata a gasar akwai Morocco da Masar da Ghana da Tunisia da Ivory Coast da Afirka ta Kudu da DR Congo da kuma Cape Verde.

Zagayen ‘yan 16
Za a fara wasannin zagayen ‘yan 32 ne daga ranar 28 ga watan Yuni, yayin da wasannin zagayen ‘yan 16 za su fara daga ranar 4 ga watan Yuli.

Za a gudanar da wasan kwata-final daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Yuli, sannan wasan dab da na ƙarshe zai gudana a ranakun 14 da 15 ga watan Yuli.

Wasan Ƙarshe
Za a buga wasan ƙarshe na gasar ne ranar Lahadi 19 ga watan Yuli a birnin East Rutherford da ƙarfe 7:00 na yamma agogon GMT.

Rahotanni sun nuna cewa wannan ne karo na farko da ƙasashe uku za su haɗa kai wajen karɓar baƙuncin Gasar Kofin Duniya ta FIFA.

Comments (0)
Add Comment