JAMB Ta Sanar Da Ranar 25 Ga Afrilu A Ranar Da Za’a Fara Jarabawar UTME

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire, JAMB, ta sanar da sabuwar ranar da za a fara jarrabawar gama-gari, UTME, ta 2023.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Fabian Benjamin a Abuja a yau Lahadi.
Benjamin ya ce UTME din, wacce da fari aka shirya za a fara a ranar 29 ga Afrilu, yanzu an janyo ta baya zuwa ranar 25 ga Afrilu, 2023.
Ya kuma ce hukumar za ta ci gaba da gudanar da jarabawar UTME ta gwaji a ranar 18 ga Afrilu, 2023.
Za a iya tunawa tun da farko JAMB ta gudanar da UTME ta gwaji ta 2023 a ranar Alhamis, 30 ga watan Maris a cibiyoyi 725 a fadin kasar nan.
Duk da haka, atisayen ya ci karo da wasu matsaloli na na’urori a wasu cibiyoyi, wanda hakan ya hana wasu ɗalibai damar zana jarrabawar.
An tsara jarrabawar ta gwaji ne da nufin gwada shirye-shiryen hukumar da na abokan aikinta na UTME tare da baiwa ɗalibai damar samun gogewa ta hanyar sanin yanayin yadda ake zana jarabawar ta na’ura mai ƙwaƙwalwa, wato CBT.

Comments (0)
Add Comment