Kamfanin jiragen sama na Emirates zai dawo da ayyukansa na jigilar fasinja tsakanin Dubai da Najeriya

Kamfanin jiragen sama na Emirates zai dawo da ayyukansa na jigilar fasinja tsakanin Dubai da Najeriya daga ranar 5 ga Disamba 2021, kamar yanda dillalan Hadaddiyar Daular Larabawa suka tabbatar a safiyar yau Alhamis.

Wannan na zuwa ne watanni tara bayan da jirgin ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya sakamakon takaddamar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu kan ka’idojin COVID-19.

Idan za a iya tunawa, a sakamakon koma-bayan da aka yi na zirga-zirgar jiragen sama bayan kulle cutar COVID-19.

Kamfanin jirgin sama mafi girma a duniya, Emirates, yace zai yi zirga-zirga zuwa ko ina daga kafofinsa na Najeriya tare da zirga-zirgar jiragen sama na yau da kullun, tare da baiwa matafiya daga Najeriya damar shiga Dubai, wanda ya kasance wurin shakatawa da kasuwanci sosai.

Comments (0)
Add Comment