Kamfanin jiragen sama na Emirates zai dawo da ayyukansa na jigilar fasinja tsakanin Dubai da Najeriya daga ranar 5 ga Disamba 2021, kamar yanda dillalan Hadaddiyar Daular Larabawa suka tabbatar a safiyar yau Alhamis.

Wannan na zuwa ne watanni tara bayan da jirgin ya dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa Najeriya sakamakon takaddamar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu kan ka’idojin COVID-19.

Idan za a iya tunawa, a sakamakon koma-bayan da aka yi na zirga-zirgar jiragen sama bayan kulle cutar COVID-19.

Kamfanin jirgin sama mafi girma a duniya, Emirates, yace zai yi zirga-zirga zuwa ko ina daga kafofinsa na Najeriya tare da zirga-zirgar jiragen sama na yau da kullun, tare da baiwa matafiya daga Najeriya damar shiga Dubai, wanda ya kasance wurin shakatawa da kasuwanci sosai.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: