Kamfanin Jiragen Saman Air Peace Ya Bayyana Shirin Sa Na kwaso ‘Yan Najeriya Da Suka Makale A Sudan Kyauta

Kamfanin jiragen saman Air Peace na kasuwanci a Najeriya, ya bayyana shirinsa na kwaso ‘yan Najeriya a kyauta, wadanda suka makale a kasar Sudan, Arewa maso Gabashin Afirka, idan har gwamnatin tarayya za ta iya samo musu filin jirgin sama mai aminci da tsaro a kowace kasar da ke makwabtaka da Sudan.
Shugaban kamfanin kuma babban jami’in gudanarwar kamfanin, Allen Onyema ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.
A cewar Allen Onyema, daliban Najeriya da sauran wadanda suka makale a kasar da yaki ya daidaita na bukatar agajin gaggawa.
Allen Onyema ya ce ya zama dole ya taimaka domin bai kamata Najeriya ta rasa ‘yan kasarta a wannan kasa ba, inda ya kara da cewa hakan zai yasa tasa gudunmawar wajen ganin an ceto ‘yan Najeriyar da suka makale a kasar wacce yaki ya daidaita.

Comments (0)
Add Comment