Karamar Hukumar Kafin Hausa ta kafa kwamiti domin yin sintirin hana fulanin Udawa lalata kayayyakin amfanin gona

Karamar Hukumar Kafin Hausa ta kafa kwamiti domin yin sintirin hana fulanin Udawa lalata kayayyakin amfanin gona da nufin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin

Shugaban KH Alhaji Muhammad Saminu Yahaya ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da kwamitin, inda ya bukaci yan kwamitin su gudanar da aikinsu bil hakki da gaskiya

A jawabinsa shugaban kwamitin ta hannun sakataren kwamitin kuma shugaban sashen aikin gona da albarkar kasa, Ahmed Tijjani ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu

Ya kuma bukaci manoma dasu kasance masu bin doka da oda domin tabbatar da zaman lafiya a fadin yankin

Kwamitin ya kunshi sarakuna da shugabannin addinai da manoma da makiyaya

Comments (0)
Add Comment