Ƙasar Jamus ta ƙulla yarjejeniya da Najeriya na maido da wasu dubban kayayyakin tarihi da aka wawushe a zamanin mulkin mallaka.
An miƙa wasu biyu daga cikin kayayyakin tarihin a wani biki a Berlin.
A shekarar 1897 ne sojojin Birtaniya suka sace tagulla daga Masarautar Benin, wato jihar Edo ta Najeriya a yau.
Daga nan aka yi gwanjon su zuwa gidajen tarihi na Turai da Arewacin Amurka, da kuma Jamus, ta biyu da ta fi karɓar kayayyakin a duniya bayan gidan kayan tarihi na Biritaniya.
Jakadan Najeriya a Jamus Yusuf Maitama Tugga ya shaida wa BBC cewa za a iya dawo wa Najeriya da kayayyakin nan da mako mai zuwa.Article