Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka

0 66

Ƙasar Jamus ta ƙulla yarjejeniya da Najeriya na maido da wasu dubban kayayyakin tarihi da aka wawushe a zamanin mulkin mallaka.

An miƙa wasu biyu daga cikin kayayyakin tarihin a wani biki a Berlin.

A shekarar 1897 ne sojojin Birtaniya suka sace tagulla daga Masarautar Benin, wato jihar Edo ta Najeriya a yau.

Daga nan aka yi gwanjon su zuwa gidajen tarihi na Turai da Arewacin Amurka, da kuma Jamus, ta biyu da ta fi karɓar kayayyakin a duniya bayan gidan kayan tarihi na Biritaniya.

Jakadan Najeriya a Jamus Yusuf Maitama Tugga ya shaida wa BBC cewa za a iya dawo wa Najeriya da kayayyakin nan da mako mai zuwa.Article

Leave a Reply

%d bloggers like this: