Kimanin mutane 14 ne suka tsere daga hannun wasu yan Bindiga a jihar Sakkwato

Kimanin mutane 14 ne suka tsere daga hannun wasu yan Bindiga, wanda suke aiki da Bello Turji, bayan sun shafe tsawon kwanaki suna tsare a hannun su a Jihar Sokoto.

Wasu Majiyoyin sun bayyana cewa mutanen sun tsere ne daga Maboyar Suruddubu, wanda take Karamar Hukumar Isa ta Jihar a ranar Asabar, a lokacin da yan bindigar suka fita aiki.

Shugaban Karamar Hukumar Alhaji Abubakar Yusif, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai ta cikin wayar tarho.

A cewarsa, ya umarci Ma’aikatan Lafiya su bawa mutanen kulawar da ta kamata, biyo bayan raunikan da suka ji a hannun yan bindigar.

Shugaban Karamar Hukumar ta Isa, ya ce 8 daga cikin wadanda suka gudun yan karamar hukumar Sabon Birni ne, 3 kuma yan karamar hukumar Isa ne na Jihar Sokoto.

Haka kuma ya ce sauran mutum 3 yan karamar hukumar Kauran Namoda ne ta Jihar Zamfara.

Kakakin rundunar yan sandan Jihar Sokoto Sanusi Abubakar, bai amsa kiran da manema labarai suka tura masa ba kan batun.

Comments (0)
Add Comment