Mai Martaba sarkin dutse Dr. Nuhu muhammad Sanusi ya bukaci gwamnatin tarayya data taimaka wajen yashe madatsun ruwan da ake dasu a fadin kasar nan.
Mai Martaba Sarki ya yi wannan kiran ne lokacin da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya kai masa ziyarar jaje dangane da mutanen da suka gamu da ambaliyar ruwa a masarautar Dutse.
Nuhu Muhammadu Sanusi ya ce fiye da shekaru 50 ke nan ba’a yashe madatsun ruwa na Tiga da Chalawa ba, wanda hakan ke jawo ambaliyar ruwa duk shekara dake lalata gonaki da rushe gidaje.
- An kara kama masu alaka da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami’ar Texas
- Gwamnan jihar Zamfara ya yi alkawarin tsai da kudurin magance ma’aikatan da ke karbar albashi da yawa a jihar
- Kifewar jirgin ruwa yayi sanadiyyar mutuwar wasu dalibai 2 a jihar Kano
- Tinubu ya nuna rashin jindadinsa kan mafi karacin albashi na Naira 615,000
- Burkina Faso ta dakatar da wasu kafafen watsa labarai da dama na Ƙasashen Yamma har sai baba ta gani
Mai Martaba Sarkin Dutse ya ce ambaliyar ruwa da ta faru a jihar Jigawa ta fi karfin gwamnatin jiha dan haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta shigo cikin wannan lamari.
Tun da farko, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace ya ziyarci fardar sarkin ne a cigaba da ziyarar masu Martaba sarakunan jiharnan domin jajanta musu dangane da iftila’in ambaliyar ruwa data samu al’ummomin su.