Ku taimaka wajen yashe madatsun ruwa don rage afkuwar ambaliya – Sarkin Dutse

0 201

Mai Martaba sarkin dutse Dr. Nuhu muhammad Sanusi ya bukaci gwamnatin tarayya data taimaka wajen yashe madatsun ruwan da ake dasu a fadin kasar nan.

Mai Martaba Sarki ya yi wannan kiran ne lokacin da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya kai masa ziyarar jaje dangane da mutanen da suka gamu da ambaliyar ruwa a masarautar Dutse.

Mai Martaba sarkin dutse Dr. Nuhu muhammad Sanusi

Nuhu Muhammadu Sanusi ya ce fiye da shekaru 50 ke nan ba’a yashe madatsun ruwa na Tiga da Chalawa ba, wanda hakan ke jawo ambaliyar ruwa duk shekara dake lalata gonaki da rushe gidaje.

Mai Martaba Sarkin Dutse ya ce ambaliyar ruwa da ta faru a jihar Jigawa ta fi karfin gwamnatin jiha dan haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta shigo cikin wannan lamari.

Tun da farko, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace ya ziyarci fardar sarkin ne a cigaba da ziyarar masu Martaba sarakunan jiharnan domin jajanta musu dangane da iftila’in ambaliyar ruwa data samu al’ummomin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: