Shugaban hukumar shige da fice ta kasa Muhammad Babandede yayi zargin cewa akwai almundahana a wata kwangilar katin shaidar zama a kasa domin kwararru ‘yan kasashen waje, wacce aka sanyawa hannu tsakanin ma’aikatar cikin gida da wani kamfanin fasaha a shekarar 2007.
Kamfanin abokin hulda ne na hukumar shige da fice ta kasa, wajen samar da katin shaidar zama a kasa domin kwararru ‘yan kasashen waje.
- Ya Kamata A Kyautata Rayuwar Talaka Bayan Cire Tallafin Mai – Atiku
- An Kama Mai Safarar Bindigogi A Tashar Mota A Zariya
- Alƙawarin Atiku Na Dawo da Tallafin Mai Ya Jawo Muhawara A Jigawa
- Tun da Na Zama Gwamnan Kaduna Ban Karɓi Bashin Sisin Kobo Ba – Uba Sani
- ’Yan Bindiga Sun Kashe Malami, Sun Sace Mutum 10 A Sakkwato
Katin shaidar tilas ne ga kwararru ‘yan kasashen waje a Najeriya. Yana basu daman su zauna tare da yin aiki a kasarnan, kuma ana iya sabunta shi kowace shekara, ko bayan shekara biyu, dogaro da shekarun aikin da aka sanya masa.
Zarge-zargen sun zo kimanin watanni goma sha takwas bayan ma’aikatar cikin gida, karkashin tsohon minista Abdurrahman Dambazau, ta kara farashin katin daga Dala dubu daya zuwa Dala dubu biyu a ranar goma sha uku ga watan Disambar 2018, biyo bayan bukatar hakan da kamfanin ya nema.