Shugaban hukumar shige da fice ta kasa Muhammad Babandede yayi zargin cewa akwai almundahana a wata kwangilar katin shaidar zama a kasa domin kwararru ‘yan kasashen waje, wacce aka sanyawa hannu tsakanin ma’aikatar cikin gida da wani kamfanin fasaha a shekarar 2007.
Kamfanin abokin hulda ne na hukumar shige da fice ta kasa, wajen samar da katin shaidar zama a kasa domin kwararru ‘yan kasashen waje.
- An tsinci gawar ƙaramin yaro a ƙarƙashin Gadar Oyun
- Kotu ta dakatar da majalisar ƙolin PDP daga cire shugaban riƙo na jam’iyyar
- Gwamnatin Tarayya ta baiwa Jihar Jigawa taki na ruwa lita 155,000 domin rabawa manoma
- Gwamnan Jihar Filato ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomin jihar
- Hukumar Zaɓe ta PLASIEC ta sanar sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Filato
Katin shaidar tilas ne ga kwararru ‘yan kasashen waje a Najeriya. Yana basu daman su zauna tare da yin aiki a kasarnan, kuma ana iya sabunta shi kowace shekara, ko bayan shekara biyu, dogaro da shekarun aikin da aka sanya masa.
Zarge-zargen sun zo kimanin watanni goma sha takwas bayan ma’aikatar cikin gida, karkashin tsohon minista Abdurrahman Dambazau, ta kara farashin katin daga Dala dubu daya zuwa Dala dubu biyu a ranar goma sha uku ga watan Disambar 2018, biyo bayan bukatar hakan da kamfanin ya nema.