Sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas,Brr. Ibrahim Hassan Hadejia ya bada gudunmawar takunkumin rufe hanci da baki guda dubu goma da dari shida da talatin ga makarantu domin rabawa daliban mazabarsa.
Wakilin Sanatan, Muhammad Lawan wanda ya mika gudunmawar kayayyakin yace hakan zai taimaka wajen marawa kudirin gwamnati baya na yaki da yaduwar cutar corona.
- Kotu ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu har sai baba ta gani
- Yan bindiga sun kai hari wani masallaci a garin Sabon Birni
- Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya kaddamar da rabon zakkar da aka tattara a kauyen Masassadi
- Ma’aikatan lantarki na Kaduna sun dakatar da yajin aiki
- NAFDAC ta buƙaci a riƙa yanke wa masu jabun magunguna hukuncin kisa
Ya kuma bukaci malamai da dalibai dasu yi cikakken amfani da shi wajen kare kai daga kamuwa daga cutar inda kuma ya yabawa ma’aikatar ilmi bisa tsare-tsaren da tayi na samun nasarar rubuta jarabawar karshen ga dalibai.
Kazalika, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ya bada gudunmawar kayayyakin bada horo ga cibiyar rubuta jarabawar kammala sakandare ta NECO dake makarantar sakandaren Famfo Goma.