Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Bauchi, Mohammed Sadiq, yayi murabus daga mukaminsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Kwamishinan a sanarwar tasa, ya godewa tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara, wanda a cewarsa shine yayi silar bashi mukamin.
- An yi bikin rantsar da Vladimir Putin a matsayin shugaban Rasha karo na biyar
- An ci gaba da ƙidayar kuri’u bayan kammala zaɓen shugaban kasa a jiya a ƙasar Chadi
- Gwamnan jihar Yobe ya jinjinawa sojojin Najeriya kan yadda suka fatattaki mayakan Boko Haram
- Jihar Borno ta yi asarar kusan kashi 53 cikin 100 na ma’aikatanta na kiwon lafiya sakamakon rikicin Boko Haram
- Najeriya za ta tsare kanta domin yaki da kasar Rasha
Hadimin Yakubu Dogara mai yada labarai, Turaki Hassan, shima ya yada sanarwar ta sa.
Wata daya baya, Yakubu Dogara, ya fice daga jam’iyyar PDP, inda ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.
Ficewar tasa daga jam’iyyar tazo ne bayan rikici tsakaninsa da gwamnan jihar, Bala Mohammed.