Kwamishina ya ajiye aiki daga shafin Facebook a Bauchi

0 190

Kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Bauchi, Mohammed Sadiq, yayi murabus daga mukaminsa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kwamishinan a sanarwar tasa, ya godewa tsohon kakakin majalisar wakilai ta kasa, Yakubu Dogara, wanda a cewarsa shine yayi silar bashi mukamin.

Hadimin Yakubu Dogara mai yada labarai, Turaki Hassan, shima ya yada sanarwar ta sa.

Wata daya baya, Yakubu Dogara, ya fice daga jam’iyyar PDP, inda ya koma tsohuwar jam’iyyarsa ta APC.

Ficewar tasa daga jam’iyyar tazo ne bayan rikici tsakaninsa da gwamnan jihar, Bala Mohammed.

Leave a Reply

%d bloggers like this: