Majalisar Wakilai ta bayyana dalilan da suka sa ta wanke Alhaji Mohammed Bello Koko

Majalisar Wakilai ta bayyana dalilan da suka sa ta wanke Shugaban Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya NPA, Alhaji Mohammed Bello Koko daga zarge-zargen badaqalar bashin naira biliyan 178 da ke tattare a rahoton yadda hukumar ta gudanar da ayyukanta na shekarar 2019.

Shugaban kwamitin majalisar wakilai da ke sauraron korafe-korafe, Hon Mike Etaba, ya bayyana mastayar majalisar a zaman bayyanar jama’a da aka yi aAbuja a makon da ya gabata.

Idan za a iya tunawa wata kungiya mai zaman kanta ta zargi hukumar da Bello-Koko a kan badakalar naira biliyan 178 na kudaden da suka makale daga basukan da hukumar take bi wadanda ke tatteare a cikin rahotonin hukumar na shekarar 2019.

A yayin da aka ci gaba da zaman sauraron matsalar na bayyanar jama’a, kungiyar ba ta bayyana ba don ta kare zarge-zargen da ta ke yi a kan haka kwamitin ya yi watsi da zarge-zargen gaba daya. Shugaban kwamitin Hon. Eytaba ya nuna takaicinsa a kan rashin bayyanar wadanda suka yi zargin don su kare tare da gabatar da hujjojin da ya kamata a kan haka ya yi watsi da zargin da suke yi wa NPA da shugabanta, Alhaji Mohammed Bello Kpko.

Comments (0)
Add Comment