Majalisun kasa suna aiki tukuru domin tabbatar da cewa yan Najeriya mazauna kasashen waje suna da damar kada kuri’u a zabe mai zuwa

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan, ya ce Majalisun kasa, suna aiki tukuru domin tabbatar da cewa yan Najeriya mazauna kasashen waje suna da damar kada Kuri’un su a lokacin zabe.

Sanata Ahmed Lawan, ya bayyana hakan a lokacin da ya karbi bakuncin Shugabar Hukumar Kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje Misis Abike Dabiri-Erewa, a ofishinsa dake Abuja.

Shugaban Majalisar ya ce majalisun kasa suna aiki tukuru domin tabbatar da cewa an samu gamsuwa a lokacin zaben.

Haka kuma ya ce suna aiki tukuru domin tabbatar da cewa yan Najeriyar da suke zaune a kasashen waje sun kada kuri’un su, kuma an Kirga su.

A cewarsa, Majalisun suna kokarin kawo sauye-sauyen a fannin zabe, ta yadda hakan zai bawa yan Kasar nan, na ciki da waje damar Kada Kuri’un su.

A jawabinsa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, kuma Shugaban Kwamatin Kawo Sauye-Sauye ga Kundin Tsarin Mulkin Kasa na shekarar 1999, Sanata Ovie Omo-Agege, ya ce an umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa INEC ta kawo sauye-sauyen ta yadda hakan zai bawa yan Najeriya mazauna kasashen waje damar zabe.

Comments (0)
Add Comment