‘Malamin makarantar da Hanifa take karatu ne ya yi gunduwa-gunduwa da ita daga bisani ya kashe ta’

Malamin Makarantar Da Hanifa Take Karatu Ne “Ya Kashe Ta”..

Wanda ake zargin Malamin Makarantar ya sanya wa Hanifa guba, inda ya yanka gawarta gunduwa-gunduwa sannan ya binne ta a cikin makarantar Private da yake gudanarwa a Tudun Wada a jihar Kano. Ya karbi kudin fansa na kimanin miliyan 6 kafin a kama shi jiya da daddare a hanyar Zaria Road dake Kano, a daidai lokacin da yake son karbar kudin fansa karo na biyu da ya nema. A cewar Malam Murtala da yaki aiki da hukumar kula da kananan yara a shafinsa na Facebook.

Comments (0)
Add Comment