Ministan sufuri na kasa ya ce ana bukatar Naira biliyan 3 domin farfado da jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna

Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ya yi hasashen harin da aka kai wa jirgin kasa, inda ya ce ana bukatar Naira Biliyan 3 domin farfado da Jirgin Kasar Abuja zuwa Kaduna.

Harin da yan ta’addar suka kai a ranar Litinin ya yi sanadiyar mutawar mutum 8 akalla.

Manema Labarai sun rawaito cewa Rotimi Amaechi ya ce sai da ya bukaci a kawo kayan aikin tsaro na zamani domin a magance aukuwar wannan ta’adin.

Mista Amaechi wanda ya yi magana da manema labarai cike da bacin rai, yana mai cewa gwamnati za ta iya magance abin da ya wakana.

A cewar babban Ministan sufurin kasar, da a ce wasu ba su hana a fitar da Naira biliyan 3 wajen sayen na’urori da kayan aiki ba, da duk wannan ba ta faru ba.

Ministan ya ce kayan aikin za su taimaka wajen tsare jirgin kasan a duk wasu wurare masu hadari.

Comments (0)
Add Comment